BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Yadda maƙwabtan Najeriya suka shiga tasku bayan cire tallafin man fetur
Ɗaya daga cikin shugabannin ƴan acaɓa a Garoua, Mamman Sani, ya ce tsadar man fetur a Najeriya ta haifar musu matsala da yawa, inda ya ƙara da cewa "idan abin bai canza ba to harkokinmu za su tsaya cak."
KAI TSAYE Ana fargabar ɓarkewar kwalara a Ukraine saboda ambaliyar ruwa
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtan ƙasashe
Arsenal na son Rice, Saudiyya na zawarcin Mahrez
Arsenal za ta sake zage damtse a zawarcin dan wasan West Ham da Ingila Declan Rice. Al Ahli ta Saudiyya na farautar ɗan wasan Algeria Riyad Mahrez daga Manchester City.
Duniya na cikin barazanar fuskantar yanayin zafi mafi tsanani a 2024
Wani abu na sauyin yanayi da aka fi sani da El Niño ya fara bayyana a tekun Pacific, kuma watakila ya kara zafi a duniyar da ke dumuma sakamakon sauyin yanayi.
Ku San Malamanku tare da marigayi Nasir Muhammad Nasir
A wannan karon cikin shirin Ku San Malamanku mun sake kawo muku tattaunawar da muka yi da marigayi limamin Masallacin Waje na Kano, Sheikh Muhammad Nasir Muhammad, wanda ya rasu a ranar 7 ga watan Yuni, 2023.
Haɗin kan da muka ba Buhari ya zame wa Najeriya matsala - Ndume
Wani jigo a majalisa ta tara ya ce yawan haɗin kan da suka bai wa gwamnatin Buhari ya sanya har sun riƙa kau da kai ga matsalolin cin hanci da rashawa.
'Ba zan manta tashin hankalin da na shiga a juyin mulkin Shagari ba'
Tsohon shugaban ƙasar ya yi mulki ne daga 1993 zuwa 1998 inda ya yi ƙoƙarin mayar da Najeriya kan mulkin dimokraɗiyya a lokacin da ƙasar ke cikin rashin kwanciyar hankalin siyasa sanadin dambarwar June 12.
Yadda wani mutum ya caccaka wa yara wuƙa a Faransa
Rahotanni sun bayyana cewa yaran ƙanana ne ƴan kimanin shekara uku da haihuwa kuma biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Gwamnatin Ghana ta hana cin nama tsawon wata ɗaya a wani yanki
Hukumomin ƙasar sun ɗauki matakin ne saboda ɓullar wata mummunar cutar numfashi da ake kira Anthrax mai matuƙar hatsari.
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Hikayata 2023: Yadda za ki shiga gasar
Wannan shafi ne da yake bayani kan yadda za ku shiga wannan gasa ta Hikayata ta 2023.
Tagwayen da likitoci suka ce ba za su wuce shekara bakwai ba sun kai 18
A halin yanzu suna kammala kwas na shekaru biyu a Kwalejin Derby kuma suna shirin yin karatun aikin jarida a Jami'ar Derby.
Muhimman dokoki biyar da Majalisar Wakilai ta tara ta samar a Najeriya
Majalisar ta yi aiki ne a wani lokaci mafi ƙalubale tun bayan komawar Najeriya kan tsarin dimokraɗiyya a 1999, saboda annobar korona da karayar tattalin arziƙin da ƙasar ta fuskanta har sau biyu a zamaninta.
Mutanen da ke rayuwa a maƙabarta mafi girma ta Kaduna
Tsawon gomman shekaru kenan yanzu, waɗannan mutanen kimanin 17 suke haƙa kaburbura da binnewa da tsaftacewa da kuma kula da maƙabartar Tudun Wada.
Za a tuhumi faston da ya sanya mabiyansa azumin mutuwa da laifin kisan-kiyashi
Mr Mackenzie ya yi wa mabiyansa fatawar cewa duniya ta zo ƙarshe, sannan ya buƙace su da su yi azumin da zai zamo silar mutuwarsu ta yadda za su haɗu da Yesu.
Me ya sa Japan ke sauya abin da ake nufi da fyaɗe?
Majalisar dokokin Japan a yanzu na tafka muhawara a kan wani muhimmin ƙuduri, wanda zai yi wa dokokin aukawa mutum da jima'i garambawul, shi ne gyara na biyu kawai a cikin shekara 100.
Ciwon sanyi na jima'i ya tsananta a Ingila
Sabbin alƙaluma sun nuna cewa Ingila na fuskantar matasalar ƙaruwar kamuwa da cututtukan sanyi na jima'i
Al'amura ba su taɓarɓare a zamaninmu kamar yanzu ba - Maryam Abacha
Abacha wanda ya rasu ranar 8 ga watan Yunin 1998, ya yi mulki ne daga 1993 har zuwa mutuwarsa lokacin da yake ƙoƙarin mayar da Najeriya kan tsarin dimokraɗiyya.
Daga Bakin Mai Ita tare da Safiya Adamu
A wannan karo cikin filinmu na Daga Bakin Mai Ita mun tattauna da ɗaya daga cikin dattijai mata na masana'antar fim ta Kannywood, wato Safiya Adamu, wadda aka fi sani da Safiya Kishiya.
Ra'ayoyin al'ummar Kano kan rusau da gwamnatin Abba ta ƙaddamar
Yayin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ƙaddamar da shirin rushe gine-gine da ta ce an yi ba bisa ƙa'ida ba, shin me al'ummar jihar ke cewa?
Budurwa mai amfani da dabarun zamani wurin gyaran mota a Kano
Halima Isa Idris ta ce babban abin da ke burge ta shi ne magance matsalar motoci, musamman a lokacin da abin ya gagari wasu.
Abin da ya kamata ku sani game da madugun adawa Ousmane Sonko
A wannan bidiyon, BBC ta yi bayani dalla-dalla kan Madugun adawar Senegal Ousmane Sonko.
Yadda tsadar man fetur a Najeriya ke cikas ga direbobin motocin haya
Yadda tsadar man fetur a Najeriya ke cikas ga direbobin motocin haya.
Za a sanar da jadawalin Premier League na 2023/24 a makon gobe
Za a bayyana jadawalin Premier League gasar 2023/23 ranar Alhamis 15 ga watan Yunin 2023.
Mac Allister ya koma Liverpool
Liverpool ta kammala sayen ɗan kwallon Argentina, Alexis Mac Allister a kan fam miliyan 35 daga Brighton.
Lerma zai buga wa Crystal Palace tamaula kaka uku
Crystal Palace ta amince da daukar dan kwallon tawagar Colombia, Jefferson Lerma kan yarjejeniyar kaka uku.
Newcastle da Man Utd na zawarcin Kim, Al-Hilal ba ta hakura da Messi ba
Mai tsaron baya a Koriya ta Kudu Kim Min-jae, na gab da daidaitawa da Manchester United da Newcastle. Al-Hilal bata hakura ba domin ta sake gabatar da sabon tayin jan hankalin ɗan wasan Argentina Lionel Messi, inda a wannan karo ta ce zata biya shi makudan kuɗaɗe har yuro miliyan 500.
Messi zai koma Inter Miami ta Amurka
Kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi zai koma taka leda a gasar kwallon kafar Amurka a Inter Miami, bayan da ya bar Paris St-Germain a kakar nan.
West Ham ta lashe Europa Conference League
West Ham United ta dauki Europa Conference League, bayan da ta ci Fiorentina 2-1 ranar Laraba a Prague.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Rana, 13:59, 9 Yuni 2023, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 9 Yuni 2023, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 9 Yuni 2023, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 8 Yuni 2023, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Daga Bakin Mai Ita Tare da Gfresh Al'ameen
A bidiyon, mawakin ya bayyana ainahin abin da ke tsakaninsa da Sadiya Haruna da kuma batun rade-radin aure tsakaninsu da ke janyo cece-kuce a kafofin sada zumunta.
Wace ce mawaƙiya Tina Turner?
An haifi Tina Turner a jihar Tennessee ta ƙasar Amurka, kuma ta fara yin fice ne a lokacin da take cikin ƴan amshi a ƙungiyar mawaƙa da mijinta ke jagoranta, wadda ake kira `the kings of rhythm`.
Shirye-shirye na Musamman
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 04/06/23
Badariyya Tijjani Kalarawi tare da Haruna Ibrahim Kakangi ne suka gabatar da shirin
Amsoshin Takardunku 03/06/23
Shin kun san me ake nufi da cire tallafin man fetur?
Lafiya Zinariya: Abin da ke haifar wa yara matsalar fitsarin kwance
A wannan makon cikin shirin Lafiya Zinariya wanda Habiba Adamu ta gabatar, an duba matsalar fitsarin kwance a tsakanin yara.
Gane Mini Hanya tare da Sanata Ibrahim Shekarau
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya ce da ya kamata sabon shugaban ƙasar ya yi wa 'yan ƙasar bayani kafin cire tallafin mai.
Kimiyya da Fasaha
Masana na ganin Ƙirƙirarriyar basira ta AI ka iya kawo ƙarshen ɗan Adam
Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta kawo ƙarshen ɗan Adam, a cewar wasu ƙwararru - ciki har da shugaban kamfanin OPenAI da na Google Deepmind.
Kumbon leƙen asirin Koriya ta arewa ya faɗa cikin teku
Koriya ta arewa ta ce wani hatsari ya afku a lokacin da take shirin aika tauraron ɗan'adam na farko a sararin samaniya, wanda ya sa ya fada cikin teku.
Yadda za ku iya gyara kuskuren da kuka yi a sakon whatsapp da kuka tura
Kamfanin ya ce za a iya gyara kuskuren da aka yi ne a cikin minti 15 bayan tura sakon.
Manhajar ƙirƙirarriyar basira ta CHatbots ta kusa ta fi mutum kaifin basira
Geoffrey Hinton ya ce a yanzu ya yi nadamar aikin da ya yi. Inda ya faɗa wa BBC cewa wasu illoli na fasahar ƙirƙirarriyar basira mai zuba zance ta (Chatbot) suna da "mugun ban tsoro".
Hotuna
Bikin nuna kayan ƙawa da wasan zamiyar teku a hotunan Afirka na wannan mako
Zaɓabbun hotuna masu ƙayatarwa daga sassan Afirka a wannan makon
Ƙayatattun hotunan auren Yariman Jordan Hussein da Rajwa Al Saif
'Yan gidan sarauta daga wurare daban-daban na duniya sun halarci taron, ciki har da Yariman Burtaniya da Gimbiyar Wales.
Domin ma'abota BBC
Africa TV
Original and high-impact BBC investigations from across Africa
A BBC Africa daily round-up of business news, with insight from African entrepreneurs
Pan African BBC discussion TV programme, exploring the life experiences of women in today’s Africa.
Weekly BBC Africa programme on health, food and lifestyle trends